Hukumar dake lura da miyagun kwayoyi wato NDLEA, sun kama wani mutum mai suna Abdullahi Sani mai shekara 40 a duniya bisa zarginsa da noma tabar wiwi a gonarsa dake kauyen Shingi a karamar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi. Kwamandan hukumar, Peter Odaudu, shi ne ya shaidawa ‘yan jarida hakan a ranar Juma’ar a yayin ganawarsa da su. Inda ya tabbatar da cewa; tabar Wiwin ita ce na biyu a mafi girma da hukumar ta kama a duk tarihin aikin hukumar a jihar.
Ya tabbatar da cewa; a ranar 5 ga watan Satumba, hukumar suka gano wurin sakamakon bayanan sirri da suka samu, inda suka je suka tarwatsa gonar. Ya ce kuma sun kama mai gonar, kuma yanzu haka yana wurinsu.