Wani mutum wanda ba a bayyana sunan sa ba ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin satar mazakuta.
An dai cafke mutumin ne a birnin Owerri n jihar Imo, bayan an same shi da laifin mamayar wani mutum yayi masa awon gaba da mazakuta. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari Zai Bayar Da Kai Bori Ya Hau, Yana Shirin Ƙara Wa’adin Tsofaffin Kuɗi
Jami’an tsaro ciki har da wani soja sune suka tasa ƙeyar wanda ake zargin da aikata laifin.
A wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta, wanda aka sacewa mazakutar ya bayyana cewa ya fita waje ne domin ɗebowa maigidan sa ruwa, a lokacin da yake dawowa sai ya ɗan dakata kaɗan ya huta.
Yace a daidai wannan lokacin ne wanda ake zargin ya mamaye shi. Ya bayyana cewa wanda ake zargin yayi amfani da hannun sa ya taɓa masa mazakuta inda nan take ta fara ɓacewa.
Bai yi wata-wata ba, nan da nan ya sanarwa da mutane halin da ake ciki, inda suka yi ta tarawa wanda ake zargin na jaki.
Yace wani jami’an tsaro shine ya shiga tsakani sannan ya ba wanda ake zargin umurnin da ya dawo masa da mazakutar sa, nan take ya tara ƙasa sannan ya faɗi wasu kalmomi kawai sai ga abar ta dawo.
Matashi Ya Samu Sauyin Rayuwa, Bayan Ya Taki Sa’ar Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Baturiya
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya bayyana irin gagarumin sauyin da rayuwar sa ta samu bayan yayi wuff da baturiya.
Wani matashi ɗan Najeriya mai suna Austino Ihezue, ya bayyana labarin soyayyar sa ga masu amfani da yanar gizo a TikTok.
Austino ya bayyana yadda talauci yayi masa katutu wanda har ya kai shi ga shan kwaki da gishiri a maimakon sukari, sannan ya riƙa tunanin ya kashe kan sa kawai ya huta