Ciniki ya fada tsakanin Manchester City da Juventus a kan Cristiano Ronaldo, kyaftin din Portugal mai shekara 36. (Jaridar AS)
Juventus ta bukaci tsakanin yuro miliyan 25 zuwa 30 (fam miliyan 21-25) a kan Ronaldo, inda ake sa ran City za ta ba shi kwantiragin shekara biyu. (Jaridar Guardian)
Pep Guardiola na kociyan Barcelona lokacin da Cristiano Ronaldo yake Real Madrid
KARANTA WANNAN LABARIN: An kurfanar da Direban a gaban Kotu bisa zargin kashe mutane 6
Kungiyar ta Italiya ta so Ronaldo ya tsaya, amma kuma rashin yardarsa ya sa take son maye gurbinsa da dan gaban Man City din kuma dan Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 24. (Sky Sports)
Paris St-Germain na kokarin sayo wasu ‘yan wasa da suka hada da Paul Pogba, na Manchester United da Faransa da Erling Braut Haaland, na Borussia Dortmund dan Norway mai shekara 21, yayin da kungiyar ta Faransa ke shirya wa kakar da za su yi ba tare da Kylian Mbappe ba. (L’Equipe)
Real Madrid ta kara kudi a tayin da ta yi na Mbappe yanzu zuwa fam miliyan 145 bayan da PSG ta ki sallama matashin a tayin da ta fara yi na fam miliyan 137. (Sky Sports)
Manchester United ta kuskure samun matashin dan wasan gaba na gefe na tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21, Noni Madueke, mai shekara 19, bayan da ya sanya hannu a sabon kwantiragi da PSV Eindhoven. (Jaridar Mirror)
Harry Kane na tattaunawa a kan sabon kwantiragi da kungiyar tasa Tottenham. Dan gaban mai shekara 28, na fatan kulla yarjejeniyar da zai rika karbar albashin fam dubu 400 a mako, bayan da ya amince ya ci gaba da zama a kungiyar ta London a bana.(Times)
Chelsea na daf da kammala daukar dan bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 22, a cinikin da ya kai na fam miliyan 42. (Sky Italia, ta jaridar Star)