Wani ango daga Miliyan wanda amaryarsa ‘yar Khanewal ta danfare shi inda ta tsere da kudinsa mai yawa a ranar Juma’ar da ta gabata, Geo News ta ruwaito.
Angon mai suna Makhdoom Rasheed, ya bayyana wurin aurensa a yankin inda ya gane cewa amaryarsa da ‘yan uwanta sun tsere.
Angon ya bayyana yadda ya biya dangin amaryar Rs300,000 wanda yayi daidai da Naira miliyan daya da duba dari shida, yayin da ake shirin kulla alaka tsakaninsu.
A shekarar da ta gabata ma an samu bayani akan yadda wani ango ya tsere ba tare da ya ba amaryarsa hakuri ba a ranar aurensu.
Labarin angon mai sunan Kallum Narton ya bazu a duniya wanda ya ki bayyana a ranar aurensa a ranar 15 ga watan Satumba. Lamarin ya faru ne a Wales da ke UK.
KU KARANTA: Amarya ta shiga damuwa: Sa’o’i kadan bayan daura masa aure, ango ya kwanta dama
Wani matashi mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rasu sa’o’i kadan bayan daurin aurensa wanda aka yi a Jihar Sokoto, LIB ta ruwaito.
Wani abokin angon, Shamsudeen Buratai ne ya tabbatar da rasuwar Lili inda yace ciwo ya kama shi. A cewar Buratai, an daura auren angon ne ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoban 2022 da misalin karfe 5 na yamma a Kofar Atiku da ke jihar, shi kuma ya rasu ranar Litinin da safe.
A cewarsa:
“Shehu, abokina tun mu na kanana kusan shekaru 30 da su ka gabata ya rasu. Yayi fama da ciwon malaria ne wanda yake kama shi duk lokacin sanya. Kamar sauran shekaru, wuraren watan Satumba ya fadi ciwon inda yasha magani kuma ya warke.
“Yau da safe da misalin karfe 9 na safe, Shehu ya fito wurinmu mun gaisa. Kwatsam sai ya fara jin wani irin ciwo a jikinsa. Sai yace yana jin alamar Malaria. Can kawai sai ya fadi, shikenan.”
Comments 1