An samu labarin wata mata ‘yar kasar China wacce ta biya bashin yaun 180,000 wanda ya yi daidai da N15.9m da ake bin angonta bayan sun hadu da wata daya, Legit.ng ta ruwaito.
Bugu da karo kuma ta bayyana cewa ta yafe masa kudin sadakin da ya dace ya biya bayan haduwarsu da wata daya.
KU KARANTA: Amarya ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda a ɗaura aurenta da angonta
Yanzu haka sun yanke shawarar yin aure ranar 31 ga watan Disamban 2022. Ta kuma bayyana cewa ta yace masa zoben daurin aure da na sa rana. Masoyin nata mai suna Hu ya yi matukar nuna farincikinsa.
Ta yanke shawarar tallafa masa da kudi makudai inda tace:
“Mun mayar masa da sadaki yaun 300,000(N19.6m) tare da ba shi wasu yaun 10,000(N651,000) don ya kai wa ‘yan uwansa. Ba son soyayya muka ba shi ba, kawai saboda ganin dacewar hakan ne.”
An samu bayanai kan yadda Hu ya tsinci kansa cikin matsanancin bashi wanda hakan yasa ta yi masa wannan tallafin.
An kwashi ‘yan kallo bayan ango ya sharara wa amaryarsa mari ana tsaka da shagali aurensu
Yayin da suka tsaya a coci suna jiran a daura musu aure, kwatsam angon ya sharara wa amaryarsa mari a fuska, Legit.ng ta ruwaito.
Da alamu amaryar bata yi zaton za ta sha mari ba, bidiyon yadda lamarin ya kasance ne @esthernice2 ta wallafa a TikTok wanda yayi matukar ba mutane mamaki.
Kafin marin an ga yadda angon ya matsa kusa da amaryar tamkar zai sunbaceta kafin daga bisani kuma hakan bai yiwu ba. Saidai bai sumbace ta ba sai ta ji saukar mari a fuska.