Jami’ai a Jamhuriyyar Nijar sun shaida cewa ambaliyar ruwa a kudu maso gabashin kasar ta tilasta wa sama da mutum dubu 20 barin muhallansu. Kamar yadda rahoton BBC Hausa ya tabbatar.
Jama’ar kauyukan sun ta amfani da buhuna cike da kasa domin kokarin toshe ruwan wanda ya taso daga Kogin Komadougou na Yobe amma abin ya ci tura.
Rahotanni sun ce tuni ruwa ya shanye wasu kauyuka da ke kusa da birnin Diffa.
Da alama idan ruwan ya janye kuma dubban mutanen da suka yi hijira suka koma gidajensu, da dama za su fuskanci matsaloli sakamakon ruwa ya lalata amfanin gonar da suka shuka.
Wannan yanki na yawan fuskantar sauyin yanayi da suka hada da karancin ruwan sama a wani lokacin kuma a samu ambaliya.
Ko a Satumbar bana sai da aka samu ambaliyar ruwa a wasu sassa na Niamey babban birnin kasar bayan Kogin Nijar ya cika taf, cikar da ba a taba ganin irin ta ba fiye da shekaru 50.
Yankin kudu maso gabashin Nijar din dai na fuskantar matsaloli na rashin tsaro sakamakon rikicin ‘yan Kungiyar Boko Haram.
‘Yan Kungiyar ta Boko Haram sun raba sama da mutum dubu 100 da muhallansu a Nijar.
Yankin ya kasance matsuguni ga dubban wasu ‘yan kasashen makwabta da suka yi hijira sakamakon makamancin rikicin.