Yadda Bishop na Katolika ya ki amsar Miliyan 25 daga Gwamna Ayade kan rashin biyan albashi
Bidiyon da ke nuna lokacin da Bishop din Katolika na Uyo Diocese, John Ebebe Ayah, ya ki amincewa da tallafin Naira miliyan 25 da Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya bayar a yanar gizo.
Gwamnan ya kasance a yayin wani taro da aka gudanar a cocin St. Patrick’s Catholic Church, Ikot Ansa, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 25 ga cocin.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Hallaka Kwamandan Ƴan Bindiga, Shanono A Harin Jirgin Kaduna
Gwamna Ayade ya yi hakan ne a wajen taron godiya ga mai shari’a Emmanuel Agim Akomaye, wanda a kwanakin baya ya samu karin girma zuwa matsayin alkalin kotun kolin Najeriya.
A cewar faifan bidiyon da ke zagayawa a shafukan sada zumunta, bishop din ya yi watsi da gwamnan da wayo ya kuma nemi ya yi amfani da kudin wajen biyan albashin ma’aikata.
Wannan ci gaban a halin yanzu yana haifar da martani a shafukan sada zumunta yayin da ‘yan Najeriya da yawa suka yaba da jaruntakarsa, inda suka nemi sauran malamai su yi koyi da Bishop Ayah.