Juventus ta doke Roma da ci 2-0 a wasan mako na 21 a gasar Serie A da suka fafata ranar Asabar.
Cristiano Ronaldo wanda ya yi murnar cikarsa shekara 36 da haihuwa ranar Juma’a shi ne ya fara cin kwallo kuma a minti na 13 da fara tamaula, sannan Roma ta ci kanta na biyu
Kwallon da Ronaldo ya ci shi ne na 25 a kakar bana, bayan da ya buga wasa uku ba tare da ya zura kwallo a raga ba.
Kuma jumulla ya yi wasa 29 a kakar 2020/21 har ma ya karbi katin gargadi uku, sai dai kawo yanzu bai ci kwallo uku rigis a wasa ba.
Kyaftin din na Portugal shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Serie A mai 16 a raga, sai Romelu Lukaku da ke biye da shi mai 14.