Ma’aikatar lafiyar Kano ta sanar da mutuwar karin mutum biyar da suka kamu da cutar Korona a jihar, yayin da kuma aka sallami karin mutum uku da suka warke daga cutar.
A daren ranar Laraba, NCDC ta sanar da mutuwar mutum biyar a dalilin annobar ba tare da bayyana jihar da suka mutu ba.
Cikin sanarwar da ta fitar da safiyar ranar Alhamis, ma’aikatar lafiyar Kano ta ce ya zuwa yanzu, jimillar mutane 427 ne suka kamu da cutar a jihar, 13 daga cikinsu sun mutu, yayin da 6 suka warke.