Wani mutum mai suna Luwizo ya gwangwanje ta hanyar auren mata 3 rigis lokaci daya.
Mutumin mai shekaru 32 da yake bayyana yadda lamarin ya faru ya ce, ya hadu da Natalie wato daya daga cikin yan uku a facebook, kuma da tafiya tayi tafiya sai suka fara soyayya.
KARANTA ANAN: NDLEA Ta Kama Wasu Yan Pakistan Da Safarar Kwayoyi A Najeriya
Bayan soyayya tayi nisa ne kuma sai suka yanke shawarar haduwa da juna domin gaisawa, wanda kuma suka shirya haduwa a tsakanin su.
Ya ce bayan ta gabatar da shi a gaban yan’uwanta mata biyun, sai suma suka kamu da son sa, wato Natasha Da Nadege.
Wizo ya ce yayi matukar mamaki lokacin da ya tambayi iyayen ta cewa yana son sauran ta, domin kuwa sun tabbatar da cewa sai dai ya dauke su baki daya domin yan uku ne.
A cewar mahaifan ta tunda dai sun kasance yan uku don haka baza a raba su ba dole ne su auri mutum ɗaya, wanda kuma zai basu kulawar da ta kamata.
Da aka tambaye shi ko yaya zai iya hada su waje daya tare da kula da su, daya daga cikin matan ta ce dolen sa ya hakura ya aure su saboda ya riga ya kamu da son daya daga cikinsu.
Ko da Lawizo ta sanar da iyayensa abunda ke faruwa sun gaya kin amincewa da fari, wanda hakan ya sa suka kauracewa zuwa bikin nasa, amma shi kuwa Ya ce baya nadamar hakan.
Matan uku dai sun kasance uwar su daya.
A wani labarin kuma: Kun yi sa’a matuƙa da kuka zama Ƴan Najeriya – Gambari ga Matasa
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce matasa sun yi sa’a da suka zama ‘yan Najeriya.
Gambari ya kuma lura cewa za a tuna da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bar tarihi na sahihin zabe da ababen more rayuwa.
Ya yi magana ne a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da mambobin kungiyar Legislative Mentorship Initiative (LMI) suka ziyarci fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.