Gwamnan jihar Bauchi ya mai da martani ga Yakubu Dogara cewa idan ɗan siyasa zai sauya sheƙa “bisa wani hasashen samun muƙami, to bai kamata ya yi ƙarya ba, bai kamata ya kawo husuma ba”.
Sanata Bala Mohammed dai ya bayyana fitar tsohon shugaban majalisar wakilan daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC a matsayin wata asara kuma abin takaici.
Yayin zantawarsa da BBC a karon farko tun bayan sauyin sheƙar Yakubu Dogara, gwamnan ya ce ana hasashen Dogara ya fita ne don neman wani muƙami don haka “ina yi masa fatan alheri”.
Ranar 24 ga watan Yuli ne, aka sanar da komawar tsohon shugaban majalisar zuwa jam’iyya mai mulki, daga bisani kuma ya dangantaka sauyin sheƙar da rashin shugabanci nagari a jiharsa ta Bauchi.
Sai dai Gwamna Bala Mohammed ya bayyana takaicin cewa bai kamata ɓatanci ya zama hanyar ban kwana kafin barin babbar jam’iyyar adawar ta Nijeriya ba.
BBC ta labarto gwamnan na cewa; “Shi yana ganin, shi ya mana alheri muka zama gwamna. Mu kuma muna ganin mu muka taimaka masa shi ma ya zama. Amma shi fa Allah, shi ke ba da mulki,” in ji Ƙauran Bauchi.