Yadda EFCC ta cika hannu da Masu Sayen Ƙuri’u a Zaɓen Gwamnan Osun
Hukumar Hana Zagon Ƙasa ta Kasa EFCC ta kama mutane uku da laifin sayen ƙuri’un mutane.
Waɗanda ta kam sun haɗa da Jimoh Kazeem, da Adeyemo Bahir, da kuma Abidogun Ismail.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ina Fatan Za A Gudanar Da Zabe Lami Lafiya –Buhari
An kama su ne a Akwatuna masu lamba ta 002 Mazaɓa ta 2, da Ababu, da Isale Osun, sa kuma Osogbo.
Haka zalika, Gidauniyar CLEEN ta yi zargin cewa Jami’an tsaro da aka turo domin kula da Zaɓen Gwamnan Jahar Osun na ranar Asabar, sun ƙyale, a yayinda wakilan Jam’iyya ke sayen ƙari’u kasa da dubu 3,000.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Cibiyar Gidauniyar ESSC ta hanyar sa hannun Muƙaddashin Darakta-Janar na Gidauniyar Ms Ruth Olofin ta sanyawa hannu.
A cewar rahoton, mutane 60 masu kula da zaɓen da an turo su ne a Ƙananan Hukumomi 30 domin duba zaɓen da yadda Jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki suka bi Dokokin zaɓen Gwamnan a Akwatuna daga lokaci zuwa lokaci.
Manajar Gidauniyar tace Mrs Chigozirim Okoro wadda ta gabatar da rahoto tace “misali a Akwati mai lamba ta 014, Mazaɓa ta 05, Cibiyar wasa ta Obafemi Awolowo daka Karamar Hukumar Ife, Magoya bayan Jam’iyya ba sayen ƙuri’un mutane Naira dubu 10,000 idan mutum zai zaɓi Jam’iyyar su.