Gobara ta tashi a babbar kasuwar garin Sakkwato, lamarin da ya janyo hasarar dukiya ta miliyoyin naira.
Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata kuma ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci.
A hukumance, ba a san musababbin tashin gobarar ba, sai dai bayanai sun ce gobarar ta soma tashi ne daga Kofar Yan Roba.
Bayanai sun ce jami’an hukumar kashe gobara na ta kokarin kashe wutar.