Wani rahoton bayanan sirri ya bankaɗo yadda gogarman Boko Haram, Kabiru Sokoto ya yi yunƙurin sace ‘ya’yan Kashim Shettima a Abuja, kamar yadda Jaridar The Cable ta wallafa a babban labarinta na Juma’ar nan.
Kabiru Umar Sokoto ya yi wannan yunƙurin ne wanda bai yi nasara ba a cikin watan Janairu, 2012, kamar yadda wasu bayanan tsaro na sirri su ka tabbatar.
Gogarman Ya nemi yin garkuwa da yaran ne lokacin da Shettima bai cika shekara ɗaya da zama Gwamna Jihar Barno ba.
Kabiru Sokoto dai shi ne gogarman da ya shirya harin bama-baman da Boko Haram su ka kai a Cocin St Theresa Catholic Church, a Madalla, kusa da Zuba a Jihar Neja.
Kuma kamar yadda hukumomin tsaro suka tabbatar, a yayin harin An rasa rayuka aƙalla 37, sai kuma mutane 57 da suka ji munanan raunuka.
Da farko dai jami’an tsaro sun damƙe shi a masaukin Gwamnan Jihar Barno da ke Asokoro, Abuja, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, duk da cewa daga bisani ya tsere daga hannun ‘yan sanda. Kuma duk da hakan an sake kama shi a jihar Taraba bayan wata ɗaya da guduwarsa, daga bisani aka sake mayar da shi Abuja.
A cikin wata takardar bayanan tsaro ta sirri da aka rubuta ranar Alhamis, 14 Ga Yuni, 2012, wadda sai kwanan nan bayanan sirrin cikin takardar su ka bayyana, Kabiru Sokoto ya yi nasarar shiga Gidan Saukar Gwamnan Jihar Barno da ke Abuja ne da niyyar sace ‘ya’yan Gwamna na lokacin, Kashim Shettima, wanda dama bai daɗe da ɗauke yaran daga Maiduguri ba, ya maida su Abuja saboda dalilai na tsaro.
Takardar sirrin wadda aka aika ta Fadar Shugaban Ƙasa, ta na ɗauke da bayanin cewa kafin Kabiru ya nemi sace yaran a Abuja, an gargaɗi Shettima cewa Boko Haram na kitsa tuggun yadda za su yi garkuwa da ‘ya’yan sa domin su samu maƙudan kuɗaɗe daga kudin fansar da zai biya dom fansar yaran sa.
Duk wannan abu da ke faruwa abun mamakin shine yadda a lokacin, Shettima bai fi watanni takwas da zama Gwamnan Barno ba.
Shettima, wanda a yanzu shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, sai ya yanke shawarar kwashe ‘ya’yan sa daga Maiduguri zuwa Abuja, Yaran waɗanda biyu mata ne ɗaya kuma namiji, an maida wasu Turkish College a Wuse, ɗaya kuma British School dake Gwarimpa.
*KABIRU YA YI SHIGAR BAREBARI* :
Rahoton bayanan sirri wanda wani babban jami’in tsaro ya sa wa hannu, ya yi zargin cewa Kabiru Sokoto ya yi shiga sanye da kaya irin na mutunen Barno, don batar da kama, kuma ta haka ne ya samu damar shiga Gidan Saukar Gwamnan Barno, inda ‘ya’yan Shettima ke zaune a lokacin.
An bada rahoton cewa ya saɗaɗa ya shige cikin gidan a ƙarshen mako, a ranar 14 Ga Janairu, 2012, lokacin da babu cinkoso da yawa.
A wani yanayi na keta dokar tsaro, Kabiru ya roƙi wani baƙo da aka rigaya aka saukar a gidan, cewa ya bar shi ya kwana a gidan, saboda shi ma baƙo ne, ba shi da masauki.
Baƙon wanda ba a bayyana kowane ne ba a cikin takardar, sai Ahmed Sanda, wanda a lokacin baya shi ne Babban Sakataren Kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno dake Asokoro, ya amince ya yi kwana ɗaya kacal.
*YUNƘURIN YIN GARKUWA A KARƁI FANSAR NAIRA BILIYAN 1*
Bayanan sirrin sun nuna cewa Kabiru ya yi niyyar yin garkuwa da yaran a ranar Litinin, 16 Ga Janairu, 2012, kan hanyar su ta tafiya makaranta.
Jami’an ‘yan sanda sun damƙe shi bayan ya kwana a masaukin Gwamnan Barno.
Shettima ya maida yaran waɗanda a cikin su babu wanda ya kai shekara 10 a lokacin zuwa Abuja, a cikin Disamba 2011, wato makonni biyu kafin yunƙurin yin garkuwa da su.
Ya ɗauke su daga Maiduguri zuwa Abuja bisa shawarar jami’an tsaro, kuma bayan an damƙe Kabiru Sokoto, an riƙa danganta cewa ba a rasa kusanci tsakanin wasun su da Boko Haram. An riƙa kuma tunanin cewa su na sanarwa Boko Haram bayanai a ɓoye.
An ce Boko Haram sun riƙa shirya yadda za su yi garkuwa da yaran domin su karɓi naira biliyan 1, wadda a lokacin kuɗin daidai su ke da dala miliyan 6.3.
*JAMI’IN TSARO GUDA ƊAYA KAƊAI*
Yaran sun bar gida wato Masaukin Gwamnan Barno zuwa makaranta a ƙarƙashin kulawar antin su mata biyu, sai kuma wani kawun su ɗaya, yayin da mahaifiyar su kuwa ta na yawan zuwa Maiduguri ta koma Abuja ne, saboda ta na zama ofishin ta na Matar Gwamna a Maiduguri.
Rahoton tsaro na sirri ya nuna cewa an yi sakacin yadda aka haɗa yaran da jami’in tsaro ɗaya tal a kullum, wanda hakan ya sanya za su iya faɗawa tarkon masu garkuwa a sauƙaƙe.
Daga baya Shettima ya ƙara yawan jami’an tsaro a Gidan Gwamnatin Barno, sai ya ɗauke yaran ya maida su makarantun kwana.
Wani babban jami’in tsaro da The Cable ta tuntuɓa, ya ce ba shi da masaniya kan bayanan sirri na 2012, wanda ke ƙunshe da bayanin yadda aka yi yunƙurin yin garkuwa da yaran.
Amma ya ce wannan zargin yunƙurin yin garkuwa da yaran, ya yi daidai da irin yadda Boko Haram ke shirya sace waɗanda su ke yin garkuwa da su.
Daga baya Shettima ya zama mutumin da Boko Haram ke so su ga sun kashe shi.
“Ban san da wannan takardar bayanan sirrin yadda aka kama Kabiru Sokoto a Gidan Saukar Gwamnan Barno ba, daga baya Kabiru ya arce yayin da aka tafi da shi a binciki gidan sa. An sake kama shi daga baya.” Inji jami’in tsaron.
“An gayyaci wasu jami’an kula da Gidan Saukar Gwamnan Barno domin a yi masu tambayoyi. Tabbas an yi bincike kan yunƙurin ta’addanci a lokacin. Gaskiyar magana dai ba a same su da laifin komai ba. Kawai dai sakaci da aikin tsaro ne kawai, wanda kaɗan ya rage da lamarin ya yi muni. Da an same su da laifi ko abin ya yi muni kuwa, to da an gurfanar da su a kotu.
“Tuna lokacin Shugaba Goodluck Jonathan, ai babu kyakkyawar alaƙa tsakanin sa da Shettima. To da a ce a lokacin an samu wani laifi kan Shettima, to sai an fallasa shi ko a kai gulmar sa ga kafafen yaɗa labarai. Tunda gwamnan jam’iyyar adawa ne a lokacin.
“Wato kawai dai lamari ne na sakarcin da har za a yi sakaci wani ya shiga Gidan Saukar Gwamna, kai ko da shi gwamnan ma ba ya ciki a lokacin.”
A ranar 20 Ga Disamba, 2013 Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke wa Kabiru Sokoto ɗaurin rai-da-rai, saboda samun sa da laifin dasa bam a cocin Madalla.