Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje ya nada Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa a matsayin sabon sarkin Rano.
Kafin dai nadin sabon Sarkin ya kasance Hakimin Kibiya kuma shi ne Kaigaman Rano.
Alhaji Kabiru ya maye gurbin Marigayi Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar III, Autan Bawo wanda ya rasu a ranar Asabar da ta wuce bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Alhaji Usman Alhaji. Sakataren gwamnatin Kano, shi ne ya sanar da nadin sabon sakin na Rano a ranar Talata.
Sanarwar ta ce an zabi Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ne a matsayin sabon sarki, daga cikin hakimai uku da suka hada da hakimin Bunkure da kuma Ciroman Rano.