Mutane 13 sun rasa rayukan su sanadiyar wani mummunan hadarin mota a Ogudumu da ke Jihar Benue.
Daga cikin fasinjojin akwai uwa da yaran ta uku wanda suka rasa rayukan su nan take sai dai daga fasinjojin akwai wanda suka tsira.
Hukumar kiyaye afkuwar hadari ta kasa road safety ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana mutuwar mutane 12 Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukan su ranar Talata sanadiyar wani hadarin mota da ya faru a kauyen Ogudumu kan titin Otukpo-Adoka a karamar hukumar Otukpo da ke Jihar Benue.
Daily Trust ta ruwaito cewa daga cikin wanda suka rasa rayukan su akwai wata uwa da yayan ta uku wanda suka nufi Abuja cikin motar haya.
Sojoji sun sada ƴan Boko Haram 8 da mahallacinsu bayan musayar wuta a Borno da Yobe Amma daga cikin mutanen da suka yi hadarin da safe, akwai wanda suka rayu.
Wani shaidar gani da ido ya ce motar wacce zata Abuja, tayi lodin fasinja daga garin Otukpo kuma ta fara tafiya lokacin da wata babbar tifa da ke zuwa daga daya bangaren da daki motar, yayin da direban ya kasa sarrafa motar kuma ta kife a Ogudumu.
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce sun mutu nan take saboda munin hadarin.
Da aka tuntube shi, babban kwamandan Road Safety (FRSC) na jihar, Mohammed Suleiman ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin mu ta wayar tarho.