Wani jirgain sama na sojoji ya yi hatsari a lokacin da yake kokarin sauka filin jirgin sama na Nanamdi Azikiwe da ke Abuja hedikwatar tarayyar Najeriya.
Mutane shida ne da matuka biyu ke cikin jirgin wanda ke hanyarsa ta zuwa Minna jihar Niger a lokacin da ya yi hatsarin sakamakon matsala da injinsa.
Ministan sufurin Najeriyar Hadi Sirika wanda ya tabbatar wa DW labarin, yace “Kawo yanzu ba wanda ya tsira a cikin jirgin”