An tsinci gawar wani mutum mazauni kasar Amurka bayan karensa ya dira kan bindigarsa wanda ake kyautata zaton shi ya ja ya rasu, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, an yi harbin ne ta kujerar baya kasancewar nan ne saitin inda mutumin ke zama.
KU KARANTA: Rayuwata yi tsada: ‘yar Najeriya ta koka kan tsadar rayuwa a UK
Wannan mummunan lamarin ya ja mafaraucin ya ji mummunan rauni wanda har ya yi sanadiyyar mutuwarsa take a wurin.
Yayin da suke cikin motar ne ake zargin karen ya dinga tsalle-tsalle wanda akwai bindigar mutumin a bayan motarsa har ya dira kanta wanda ya janyo harbin.
Mutumin asali dan Kansas ne da ke cikin Amurka, kuma yana kan hanyar zuwa farauta ne tare da karensa wannan ibtila’i ya afka masa.
An tabbatar da cewa mutumin na kujerar da yake tuka mota ne yayin da karensa yake kujerar baya lokacin da lamarin ya auku.
‘Yan sanda sun bayyana yadda yake kan hanyarsa ta zuwa farauta inda ya bar karen a kujerar baya, ashe tsautsayi zai gifta.
Kamar yadda suka bayyana, mutumin mai shekaru 32 ya rasu ne ranar Asabar, 21 ga watan Janairun 2023.
An samu bayanin yadda yadda karen yake tsalle-tsallensa ya afka kan bindigar daga nan ya yi sanadin mutuwar mafaraucin.
Hotunan matashin da ya yi ankon suttura da kare, ya sanya shi a gaban mota ya ɗauki hankula
A wani guntun bidiyo, an ga yadda wani matashi da kare suke kwasar rawa a cikin wata mota yayin da suke sanye da suttura iri daya, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da wata waka ke tashi, an ga yadda mutumin ke kambama karen yayin da karen ya cigaba da gyada kai ga kidan.
Mutane da dama sun yi mamaki yayin da suka dinga tsokaci kan yadda karen ya dinga yin abubuwa kamar mutum.