IMG-20200120-WA0034

Yadda Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Ganduje A Matsayin Gwamnan Kano

Kotun koli ta tabbatar da nasarar Abdullahi Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano. Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf shi ne ya shigar da kara a gaban kotun kolin yana mai kalubalantar zaben ranar 23 ga watan Maris da ya gudana a wadansu mazabu a jihar Kano.

Alkalai bakwai na kotun koli wanda Babban mai shari’a na Nijeriya, Tanko Muhammad ya jagorance su, bayan sauraren korafin mai shigar da kara da wanda aka shigar, sai ya sanya yau Litinin a matsayin ranar yanke hukuci.

A hukuncin da mai shari’a Sylvester Ngwuta na kotun kolin ya yanke, ya yi watsi da karar na Abba Kabir Yusuf wanda yake kalubalantar zaben Gwamna Ganduje a matsayin korafi mara tushe. Kotun ta ce wanda yake kara ya kasa gamsar da kotun da hujjoji wanda ke nuni da cewa zaben ranekun 9 da 23 ga watan Maris din 2019 bai inganta ba.   

A ranar 9 ga watan Maris din 2019 ne, hukumar zabe mai zaman kanta na Nijeriya wato INEC ta ayyana zaben 9 ga watan Maris na gwamnan jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba. Inda ta sake gudanar da zaben a wadansu mazabu a ranar 23 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *