Liverpool ta lallasa kungiyar Racing Genk da ci 4-1 a gasar kofin Zakarun Turai a jiya Laraba. Duk da wannan nasarar da suka samu, amma mai horas da ‘yan wasan wato Juergen Klopp ya ce bai ji dadin wasan ba.
Alex Oxlade-Chamberlain, ya zura kwallo biyu, a wasan shi na farko cikin wata 18, inda shima Sadio Mane da Mo Salah suka zura kwallo guda-guda.
Mbwana Samatta ya ci wa Genk kwallo dayan da suka samu tun kafin a je hutu zangon farko, kafin daga bisani Liverpool su zo su yi nasara.
Yanzu haka ‘yan wasan Klopp din sune na daya a rukuni na E, inda suke da maki shida a sama da Napoli da maki 1.