Wata mata mai suna Aba ta bayyana cewa ta samu ciki kuma ta haihu amma a saninta babu namijin da ya taba saduwa da ita, Wonder9ja.com ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da Barima Kaakyire Agyemang a Step1 TV, matar ta ce shekaru hudu kenan da ta san cewa babu namijin da ya taba ko rike hannunta balle su kai ga saduwa.
KU KARANTA: Kwamacala: Ƙasashe 4 da mata ke iya auren maza fiye da ɗaya
A cewarta ko da taji ciwon cikin ta yi tunanin fibroid ne ba juna-biyu ba. Yayin da ta isa asibiti, ta ce an bukaci yi mata aiki don cire abinda ke cikinta.
Ta kara da cewa ta yi iyakar kokarinta na turo fibroid din saboda tsoron kada ayi mata aikin amma ga mamakinta sai santalelen jariri ya fito.
Matar wacce ke siyar da ruwa a bakin-titi ta cigaba da shaida cewa ba ta da kudin kulawa da jariri a halin yanzu.
Saidai akwai matar wani fasto da take ta kulawa da yaron tun sanda aka haife shi har yanzu tana iyakar kokarinta.
Cigiya: Attajirar mata a Abuja tana neman kyakkyawan namijin da zai ɗirka mata ciki ta ba shi N3m
Wata mata mai dukiya da ke zama a garin Abuja wacce bata taɓa haihuwa ba tana cigiyar namiji mai kyau da zai ɗirka mata ciki, Legit.ng ta ruwaito.
Wata fitacciyar ma’abociya amfani da shafin sada zumuntar zamani, Uwaoma Susan Joseph ce ta bayyana wa duniya wannan kudirin na matar a Facebook inda ta adana bayani akanta saboda tsaro.
Yayin da matar take nema, ba kyauta zai yi mata wannan gagarumin aikin ba, akwai Naira miliyan uku (N3,000,000) da ta yanke shawarar za ta bai wa wanda ya cancanci su yi wannan harkar da shi kuma ya aiwatar da komai lafiya.