Wani mutum a Twitter mai suna @makavelli275 ya bayyana labarin yadda matasa uku su ka je har garin Abuloma da ke Port Harcourt, Jihar Ribas inda su ka zabo matan aure, LIB ta ruwaito.
KU KARANTA: Shekarar da ta gabata warhaka muna shagalin aurenmu, Matashi na makokin rasuwar matarsa
A cewarsa har yanzu su na nan zaune daram da matansu yayin da ya bar kasar. Ya bayyana cewa:
“Lokacin ina zama a PH ( Wato a garin Abuloma), na san wasu samari uku a garin wadanda su ka je har gidan karuwai da ke garin su ka zabo matan aure.
“Kuma har lokacin da na bar kasar suna nan tare. Sannan har yanzu ban san dalilinsu na yin hakan ba.”
Yayin da masoya ke taya Halima Atete murna, har wasu sun kula da hujin da ke jikin mayafinta ranar aurenta
A ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba ne aka sha shagalin auren fitacciyar jarumar Kannywood Halima Atete.
Cincirindon jarumai mata da maza sun je bikinta wanda aka sha shagulgula iri-iri cike da al’adun Kanuri wato mutanen Maiduguri.
A hotunanta da su ka bayyana, an ga yadda jarumar taci kurus ta sanya kayan alfarma kuwa ta dauki kwalliyar kece raini.
Babu wata alamar makusa, kuma ko da wakilin Dimokuradiyya be je bikin ba amma ko da gani wurin ya dauki kamshi kasancewar haka al’adar mutanen Maiduguri take.