Lokacin Kirsimeti lokaci ne da Kiristoci suka keɓe don yin bikin haifuwar Yesu Kiristi. Yawancin lokaci ana yi masa alama ta hanya ta musamman. Ga Kiristoci, babu wani lokacin bukukuwa da aka jera sama da shi musamman yayin da ake shiry-shiryen shiga da sabuwar shekara. Har ila yau, a cikin wannan lokaci, yawancin ‘yan Najeriya suna tafiya don asaline garuruwa su, donmin yin bikin tare da ‘yan uwansu.
Sai dai wasu mazauna birnin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun nuna damuwarsu kan hauhawar farashin kayayyakin abinci, a lokacin bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara.
A cikin wani shirin na gidan Talbijin din Trust TV, sun zaga kan titunan Abuja domin jin yadda mazauna Abuja ke shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti a cikin halin kunci da tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta, inda mutane suka Koka game da matsalolin rashin kudi da kuma tsadar rayuwa.