Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya angwance inda aka yi bikinsa a Turkiya.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ne babban abokin ango a bikin na Ozil da aka gudanar a ranar juma’a.
Dan wasan na Arsenal mai shekara 30, ya auri amaryarsa ne tsohuwar sarauniyar kyau ta Turkiya Amine Gulse a wani babban otel a Istanbul na Turkiya.
Ma’auratan sun fara soyayya ne tun 2017, kafin su sanar da za su yi aure a watan Yunin 2018.
Ozil dai dan asalin Turkiya ne, kuma Bajamushe, inda yake wakiltar Jamus a kwallon kafa.
Ozil ya sanar da yin ritaya daga buga wa Jamus kwallo bayan ya suka kan wani hoto da ya dauka tare da shugaba Erdogan.