Wata mata mai suna Habiba Hamidu ta bayyana yadda mijinta ya lakada mata bakin duka bayan ya kamata dumu-dumu tana hira da wani namiji a Facebook.
Kamar yadda bidiyon hirar ta da At-Tasfiyya TV ta yi da ita, an ga yadda fuskarta ta ci duka inda ta kumbura ta yi suntum ta yadda ba za a iya gane asalin halittarta ba sakamakon dukan da taci a hannun mijinta.
KU KARANTA: Jami’an KAROTA sun kama wani jaki dea ke gararamba a titin Kano
Ya bayyana cewa bayan shigowa dakinta ne ya tambayeta da wanda take hira a waya, sai ta bayyana masa cewa da abokinta na Facebook take hira.
A cewarta sanar da shi ke da wuya ya hau dukanta kamar Allah ya aiko shi, inda ya ce dama ya yi zargin da namiji take hira.
Ya ce ba wata alaka bace babba tsakaninta da wanda take hirar da shi, kawai a Facebook ne ya tura mata goron gayyatar zama kawarsa ita kuma ta amsa daga nan hira ta yi tsawo tsakaninsu.
Ta bayyana cewa abinda ya sa take neman wanda za ta yi hira da shi saboda tana yawan samun matsala da mijinta ne, kuma sam ba sa hira.
Kasancewar dare ne sosai, sai ta bukaci ta nemi wanda zai debe mata kewa, hakan yasa ta biye wa matashin suka dinga kwasar hira.
Ta ce shekarunsu 10 da aure da mijinta, kuma Ubangiji ya azurta ta da yara guda 4. Ta kuma shaida yadda dama yake dukan maza tun kafin ya aureta idan ya ga suna magana da ita.
Ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da ya dake ta tun bayan auren, na farko saboda ta fita bata dawo gida da wuri bane, sai wannan karon na biyu.
Yadda karuwa ta lakaɗa wa abokiyar sana’arta na jaki kan yi wa kwastomomi rahusa
Mariam Imodia ta bayyana gaban kotun majistaren Mombasa, wanda a gaban alkali Vincent Adet ta amsa laifin azabtar da Gladys Ahela.
An samu bayani kan yadda Ahela ta koma yankin Saba Saba da ke Mombasa Central Business District (CBD) a Kenya, bayan wasu kwastomomi da suka kai mata ziyara.