Mawakiya Shania Twain ta bayyana cewa tana danne albarkatun kirjinta saboda gudun mijin mahaifiyarta, Jerry Twain ya lalata ta a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba, LIB ta ruwaito.
Mawakiyar mai shekaru 50 ta ce Jerry Twain ya kasance yana cutar da ita yayin da take zama a gidansa kamar yadda The Sunday Times ta ruwaito.
KU KARANTA: Yadda Sule Ɗan achaɓa ya cika bujensa da iska bayan budurwar da suke lalata ta sheƙa lahira
Ta cigaba da cewa:
“Ina boye kaina tare da danne albarkar kirjina. Ina sanya rigunan maman da suka yi min kadan.
“Wani lokacin har guda biyu nake sanyawa sannan in danne su yadda babu wani tudun jikin mace da zai bayyana a jikina. Hakan ya fi min sauki. Saboda ba za ka so zama mace a gidanmu ba.”
Twain ta fara wakoki tana da shekaru 8 da haihuwa inda ta dinga fama kafin ta amince cewa I ta mace ce saboda azabtarwa.
Ya bayyana yadda aka dinga cutar da ita a wani labarin rayuwarta da ta bayar a 2011, mai suna “Daga wannan Lokacin.”
A cikin littafin, Twain ta bayyana cewa akwai lokutan da rikici ke hautsinewa tsakanin iyayenta har ta dinga tunanin mijin mamarta zai halaka mata uwa. Iyayenta sun rasu ne a lokacin tana da shekaru 22 da haihuwa.
Matasa sun lakaɗa wa shugaban makarantar sakandare na-jaki bayan kama shi yana lalata da dalibarsa
Matasa sun kama wani mataimakin shugaban makarantar sakandare dumu-dumu yana lalata da dalibarsa, LIB ta ruwaito.
Mutumin wanda shi ne na biyu a matsayi a makarantar sakandare nan Kgagatlou da ke Polokwane, Limpopo ya ci na jaki bayan an kama shi yana lalata da dalibarsa yayin da wasu daliban ke karatu a azuzuwansu.
A wani bidiyo da ya dinga yawo a Twitter, sai da suka daure shi jikin ice sannan suka dinga dukansa kamar Allah ya aikesu.