Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana yadda ya hana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yin tazarce. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Yan takarar yan majalissu a inuwar Jam’iyar da ya gudana a daren ranar Lahadi a Babban birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
A cewar Atiku ” A lokacin da na ke mataimakin shugaban kasa, na samu kyakkyawar fahimtar juna tsakani na da mambobin majalissar kasar nan, kuma wannan alakar ce ta bani damar tsayar da matakin Obasanjo na ci gaba da mulki a karo na uku
“A shirye nake na tabbatar kun sake bada ta ku gudunmawar idan kuka sake dawowa majalissa kamar yadda kundin tsarin mulki ya baku dama domin cigaba da bunkasa Dimokuradiyya da samar da cigaba ga Kasar mu”
Kazalika dan takarar jam’iyar na PDP ya kuma bayyana takaicin sa kan halin rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki da kasar nan ke ciki, yayin da ya bayyana cewa, ” An raba kawunan mu fiye da da, sakamakon ayyukan da tsare-tsaren Gwamnatin Jam’iyar APC”
A wnai labarin kuma, Gwamnatin Katsina Ta Bukaci Maninyata Aikin Hajjin 2023, Su Kawo N2.5m
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware ma jihar Katsina guraben kujerun aikin hajjin 2023 guda 4,913. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu-Kuki, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Katsina lokacin da yake zantawa da manema labarai.