Wani Dan Shekaru 13 a ranar Litinin 20 ga watan Satumba, ya shaida ma wata Kotun Kenya dake Nairobi, yadda ya rika lalata da yar aikinsu mai shekaru 32 na tsawon watanni8
Yaron ya tabbatar da haka, bayan an bada belin yar aikin, inda yace tarayyar su ta fara ne tun watan juli na Shekarar 2020, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
Ya shaidawa Kotun cewa, cewa yayi lalata da yar aikin wadda sunanta V.N.W na akalla sau 3 a sati daya, inda yace hakan na faruwa ne a tsakanin karfe 1 na rana, zuwa karfe 4 na rana a wannan kwanakin da suke lalata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: An tsaurara Tsaro a Abia yayin da kotu ke sauraren karar Nnamdi Kanu
Ya kara dacewa, ” ta gaya mani cewa sirrin mu ne Kuma kada in gayawa kowa, a dalilin haka, ban taba gayama iyaye na ba, har sai lokacin da aka kama ni, ina kallon bidiyo na batsa ta amfani da wayar yaya ta.
Yaron yace yana kamuwa da sha’awa, a duk lokacin da ya kalli bidiyo na batsa, kuma suna yin lalatar a wajen dafa abinci-kitchen ko kuma dakin da ake hutawa bayan kowa yayi bacci.
Ya kara dacewa, yace ya saci wayar yayar tashi ba tare data sani ba, domin cigaba da kallon bidiyon.
Minor yace yar aikin tana yawan gaya mashi cewa, abunda suke aikata babu kyau, amma bai daina ba.
A lokacin da aka tambaye shi idan tilasta mashi akayi ya aikata lamarin yace, “a’a. Ni ke jin ina son inyi sai na cire wando na ba tare da tilasta mani ba, sai muka yi shi tunda farko.”
An kama V.N.W gami da tuhumar ta da lalata karamin yaro dan Shekara 13 na tsawon watanni 8, tare da koyawa yaron aikata abubuwan batsa a watan Fabruri na Shekarar 2021.
A wannan lokacin, an zargi V.N.W a matsayin wadda ta aikata laifin a yankin Mwika na Kasarani dake Nairobi, a tsakanin juli na Shekarar 2020 zuwa Fabruri na Shekarar 2021.
An tuhume ta da koyawa karamin yaro kallon bidiyo na batsa da lalata Minor inda yanzu ya saba aikata jima’i.
Takardun da aka gabatar a gaban Kotun, sun tabbatar dacewa, iyayen basu boye lamarin ba, domin sun hukunta shi akan lamarin a ranar 21 na watan Fabruri.
Yar uwar yaron ta yi korafin cewa, ta rasa wayar ta a gidan su. Bayan ta tambayi yayyan ta, amma dukkanin su, sun karyata satar wayar, inda ta bukaci iyayenta akan su shigo lamarin.
A lokacin da aka buge shi, yaron ya tabbatar da amfani da wayar yayar tashi wajen kallon bidiyon aikata jima’i, bayan yar aikin ta koya mashi, inda aka yi saurin kaishi Asibiti kafin a shaidawa Yan sanda.
Yan sanda sun tabbatar dacewa, yar aikin ce ta fara nuna mashi bidiyo na aikata jima’i. Wannan lamari ya cigaba da faruwa har zuwa lokacin da ta fara lalata da Minor da kanta.
Wanda ake zargin ta ki amince wa, inda aka bada ita beli, tare da dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Satumba na Shekarar 2021.
Toh yaruwa kenan