Wani ɗan Najeriya wanda yake zaune a ƙasar Turkiyya, ya kama wacce zai aura tana sheƙe ayar ta a otal.
Asirin budurwar ya tonu ne a cikin wani gwajin riƙon amana da wata mai ɗaukar bidiyo mai suna Sonia ta haɗa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bidiyon gidan da ake biyan N800k a shekara ya ɗauki hankula
Sonia ta sanya bidiyon yadda cakwakiyar ta kasance a tsakanin masoyan biyu a shafinta na Facebook.
A cewar Sonia, matashin yana turowa budurwar ta sa kuɗin kula da kanta kowane wata, sannan ya buɗe msta shagon sayar da kaya na N6.5m a Najeriya, amma ta yarda ta ƙarbi dubu ɗari da hamsin domin a sheƙe aya da ita a otal.
Sheƙe ayar dai za ayi ta ne da mace ƴar’uwarta, sannan ta amince da su haɗu da Sonia a otal. Amma tana isowa maimakon ta ga wacce zata sheƙe ayar da ita sai ta ga saurayin ta.
Cikin kaɗuwa budurwar ta fara magiya tana ƙoƙarin ƙirƙiro ƙarerayi domin ta wanke kan ta, amma saurayin na ta sam ya ƙi yarda da ita.
Abubuwa sun rincaɓe inda tayi ƙoƙarin huce fushin ta akan Sonia ta hanyar kamata da faɗa.
Sonia ta bayyana cewa a 13 ga watan Fabrairun 2023 aka shirya gudanar da auren su.
Abun Al’ajabi: Tagwaye Sun Samu Juna Biyu a Tare, Sun Haihu Lokaci Ɗaya
A wani labarin na daban kuma, wasu tagwaye sun samu juna biyu a tare, sun haifi jariran su lokaci ɗaya.
Wasu tagwaye sun ɗauki hankunan mutane a yanar gizo bayan bayyanar bidiyon su inda aka nuna cewa sun haihu a tare.
Bidiyon wanda ya karaɗe yanar gizo ya nuna kyawawan jariran da tagwayen suka haifa.
Bidiyon wanda wata mai amfani da @itsterrilyn ta sanya a manhajar TikTok, ya nuna tagwayen daga farko, kafin daga bisani aka nuna kyawawan jariran da suka haifa.