Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasa, Sanata Abdullahi Adamu murnar cika shekaru 76 da haihuwa.
Shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawun sa Femi Adesina ya fitar a ranar Asabar, ya bi sahun kwamitin zartarwa na kasa (NEC), kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da daukacin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki domin yin bikin taya shi murna.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya kawo hangen nesa da jajircewa ga dimokuradiyya da gudanar da mulki a kasar nan, inda ya shiga harkokin siyasa a shekarar 1977 a matsayinsa na dan majalisar wakilai wanda ya taimaka wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar nan 1979.
Ya kuma kasance memba a taron kwamitin tsara kundin Tsarin Mulki a 1994.
Ya kuma yaba wa shugaban jam’iyyar APC na kasa kan yadda ake ci gaba da sake mayar da jam’iyyar bisa turbar sulhu, tare da kara mayar da hankali wajen karfafa tsarin dimokuradiyya na cikin gida, samar da kyakkyawan shugabanci da aiwatar da aikin tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya.
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya kara lafiya da karfin gwiwa ga Sarkin Yakin Keffi da Aare Obateru na Ife.