Mista Abraham Ani, wani matashi ne daga ƙaramar hukumar Ezza dakw jihar Ebonyi an harbe shi a ƙafa yayin wani rikic da ya ɓarke tsakanin rundunar soji da kuma al’ummar dake rajin kafa ƙasar Biyafara a jihar Enugu. Ani ya bayyanawa Raphael Ede a wata tattaunawa ta musamman cewa an harbe sa ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa majami’a.
Rahotanni sun bayyana cewa soja ne ya harbe ka a ranar 23 ga watan Agusta, 2020, me ya jawo hakan?
Ni dai ina zaune ne a Eneme dake ƙaramar hukumar Enugu ta gabas, na shirya na fito daga gida da niyyar zuwa majami’a domin yin ibada, akan hanyar zuwana sai naga mutane na dawo wa, nan take na tsayar da mutum ɗaya daga cikinsu, na tambayesa abinda yake faruwa sai ya shaida min cewa malamin majami’a ne yace kowa ya koma gida saboda ba lafiya, sai nima nayi amfani da maganar wannam mutum dana tambaya, na juya ina tafiya sai na ga mutane na gudu, can sai na hango sojoji na binsu da harbe ban ɓata lokaci ba nima sai na ɓuya a bayan wata mota. Nan take sojan da ya hango sai yazo inda nake yace na fito, ban fito ba sai ya dinga ja na a ƙasa, sai nace masa wane irin laifi na aikata, shin ko laifi ne mutum ya ɓuya a yayin da yaga ana harbe-harbe, wani soja ɗan uwansa na zuwa inda muke sai ya ba shi umarnin ya rabu dani amma bai ƙyale ni ba sai kawai ji nayi ya harbe ni a ƙafa.
Su wane suke gudu yayin da sojojin suka biyo su?
Abinda na fuskanta shi ne mazauna yankin ne da suke ɗaukar Bidiyon abinda sojojin ke aikata.
Me ya faru bayan nan?
Harbe-harben da mutane suka ji shi ya ja hankalinsu domin zuwa su ga me yake faruwa, a nan suka tarar dani cikin jini basu ɓata lokaci ba suka ɗauke ni zuwa asibiti.
Kana da masaniyar cewa akwai wani rikici da ya ɓarke tsakanin jami’in tsaro da kuma al’ummar dake rajin kafa ƙasar Biyafara a makarantar Eneme a wannan safiya?
Bani da labarin faruwar wani abu, dana sani ba zan fito ba zan yi zamana a gida nayi addu’a, sai bayan na fito ne na fuskaci cewa wani abu na faruwa.
Zaka iya gane sojan da ya harbe ka?
Ba zan gane shi ba, amma daga jin yanayin harshensa nasan Bahaushe ne.
Ka sanarwa da hukumar ‘yan sanda abinda ya faru da kai?
Ina asibiti lokacin likita yana wanken min ciwon, wasu ‘yan sanda suka zo suka bani haƙuri da cewar na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara. Bayan wani lokaci ma wasu ‘yan sandan suka sake zuwa suka yi min tambayoyin yadda lamarin ya faru, na sanar da su komai har na nuna musu katin shaidar inda nake aiki a Emenite, su ma suka bani haƙuri.
Aikin me kake yi a Emenite?
Ni ina ɓangaren da ake sarrafa kwanon da ake rufin gida ne.
Ta ya aka yi kazo asibitin ƙashi na tarayya dake Enugu?
A lokacin dana ke asibiti a Eneme daga ranar 23 zuwa 26 ga watan Agusta, likitan da yake kula dani yace gaskiya ba zai iya yin magani a wannan asibiti ba saboda harsashin da aka harbe ni ya shiga cikin ƙashi na sosai, dan haka ya tura ni asibitin ƙashi ja tarayya, ba jimawa sai ga wasu ‘yan sanda wai zasu kai ni asibitin ƙashi, nace ba zan bi su ba in har babu wani ɗan uwana a a tare dani, nan take na kira wani ɗan uwana muka shiga motarsu, abun mamaki sai suka wuce dani ofishin bincike a maimakon inda likita ya tura ni. Ina cikin motar a zaune sai wani ɗan sanda mai suna Henry shi da abokin aikinsa suka shiga ofishin shugaban hukumar ‘yan sanda, Ahmed Abdurrahman.
Bayan fitowarsu daga ofishin ban san me suka tattauna ba, sai suka sameni suka ce na godewa Allah domin ba dan sun yi bincike sun gano bani da laifi ba da sun yi magani na, nace musu a koda yaushe ina tare da Allah. Nan take suka ɗauke ni zuwa asibitin ƙashi na tarayya dake Enugu. Bayan sun kai ni na ɗauki wasu ‘yan kuɗaɗe na basu, sannan muka yi musayar lambar waya. Washegari da safe sai Henry ya sake dawowa ya saka min ankwa a kafa, na tambayesa dalilin yin hakan yace shugaban hukumar ‘yan sanda ne ya bashi umarnin yin hakan. Bayan da aka zo za a yi aikin ƙafar na kirasa nace su zo su cire min, shi ne yazo ya cire bayan yin aikin kuma ya sake saka min ankwar.
Wane yake biya maka kuɗin magani?
Ni nake biyawa kaina kuɗin magani dana asibiti, idan baka manta ba na faɗa ma cewa ‘yan sandan nan sun ce na godewa Allah, saboda bayan faruwar lamarin an kashe mutane da dama, yanzu gashi bani da kuɗi ƙarfina ya ƙare, sai dai nayi kuka dare da rana domin neman ɗauki, dalilin da yasa ma nake samun abinci saboda asibitin ne ke bayarwa kuma shi ma yana cikin kuɗin da zan biya.
Tun da jami’an ‘yan sanda suka ce suna bincike akan lamarin, sun ɗauki rahotonka ne?
Tun ranar 26 ga watan Agusta sai uku kaɗai ɗan sanda ya zo wajena, na farko yazo ya samin ankwa, na biyu kuwa ni na kirasa akan ya cire min ankwar akan za a min aiki sai kuma na karshe da yazo ya sake mayar min da ankwar ya kuma karɓi lambar wayar mai gidana.
Yanzu mene buƙatarka?
Abinda nake so shi ne ‘yan sanda su cire min ankwar da suka saka min, sannan su san cewa ni ba mai laifi bane kuma bana tare da wata ƙungiya, kuma su ɗauki nauyin kula dani har na warke.