Ana zargin Sule ya kebe da budurwa mai suna Muniat a ranar Juma’a da dare, amma kuma aka neme shi aka rasa bayan an ga gawarta a karamar hukumar Igbogbo Bayeku da ke Jihar Legas, Nigerian Pulse ta ruwaito.
An tattaro bayanai ka yadda mai kula da masaukin bakin ya duba dakuna kamar yadda ya saba inda ya tsinci gawar Muniat.
KU KARANTA: Saurayina yana ba ni sama da N11m duk don gyara kaina, Budurwa
Bayan ganin hakan ne yasa mai kula da masaukin bakin yayi gaggawar sanar da caji ofis din Ikorodu, bayan nan ne jami’an ‘yan sanda su ka ci gaba da bincike.
A bayanin da yayi, kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya shaida cewa jami’ansu sun je wurin inda su ka tabbatar cewa babu wata alamar azabtarwa a jikin Muniat.
Kamar yadda takardar ta nuna:
“Manajan masaukin bakin ya kira ofishin ‘yan sanda da misalin karfe 6 na safiyar Asabar inda aka sanar da cewa an tsinci gawar wata mata da aka kawo ta rasu a masaukin baki a ranar Juma’a da dare.
“An gano matar mai shekaru 46 mai suna Muniat, mutumin kuma Alfa Sule. Ya shigo masaukin baki da wani babur.”
Yadda budurwa ta kai karenta wurin budurwarsa (karya), take su ka cika da shauƙin juna
Wata budurwa ta wallafa gajeren bidiyonta wanda ta sanya karenta cikin shayin bayan kai shi wurin budurwarsa a makwabtansu, Legit.ng ta ruwaito.
Yayin da ta mika shi wurin karyar, nan da nan su ka fuskanci juna cike da shauki, wanda wannan bidiyon yayi matukar daukar hankalin jama’a.
Budurwar mai suna @itemeleng_belinda, ta bayyana had da ta bar karenta ya je inda yake so da kansa.
Bayan sakanni ke dan a cikin bidiyon sai ta gane cewa wurin budurwarsa yake son zuwa. Karnukan sun kamu da soyayya juna, dukkan alamu na nuna hakan.