Ganawar da aka yi tsakanin Ministan Sufuri, Mista Rotimi Amaechi da kungiyar ma’aikatan jiragen kasa ta Najeriya kan yajin aikin gargadi na kwanaki uku da suka shirya an tashi baran baran ba tare da cimma matsaya ba.
Kungiyoyin sun ayyana yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga ranar Alhamis 18 zuwa 20 ga watan Nuwamba domin neman karin albashi.
Wata wasika mai suna, “Sanarwa da Umarnin shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 3 a fadin kasar nan,” mai kwanan wata 12 ga watan Nuwamba, an aika wa shugaban gundumomi/Sakataren kungiyar ma’aikatan jirgin kasa da kungiyar manyan ma’aikata ta Najeriya.
Sai dai a lokacin da aka gayyaci kungiyoyin kwadagon a Abuja, an gano cewa Ministan ya bukace su da su janye yajin aikin kafin a fara wata tattaunawa inda kuma suka yi watsi da bukatar.
Babban sakataren kungiyar ma’aikatan jiragen kasa ta Najeriya (NUR), Kwamared Segun Esan, a wata zantawa da ya yi da wakilinmu, ya tabbatar da cewa za a ci gaba da yajin aikin, yana mai cewa bukatar ministan aiki ne da ba zai taba yiwuwa ba.