By Abbas Yakubu Yaura
Gbata, daya daga cikin tsofaffi kuma mafi girma a karamar hukumar Wamba ta jihar Nasarawa, ya shafe shekaru da dama yana fama da matsalar rashin samun ruwan sha sakamakon rashin samun rijiyar burtsatse.
Binciken da Aso Chronicle ya yi ya nuna cewa mazauna Gbata, musamman mata, suna yin tattaki mai nisa domin neman ruwan sha a kowacce rana.
Sai dai a makon da ya gabata ne aka kawo musu dauki sakamakon kokarin da wata bazawara mai suna Mama Zainab Ishaku ‘yar shekara 75 ta yi, inda ta hada hannu tare da karfafa gwiwar mata a cikin al’umma da su rika ajiye wani bangare na kudadensu na Canjin kudi da suke samu na naira 5,000 duk wata domin gyara rijiyar burtsatse.
A lokacin da Aso Chronicle ta ziyarci al’ummar yankin, ta lura cewa matan sun girka tankunan ruwa da famfo a wurare masu muhimmanci kamar makarantar firamare ta gwamnati daya tilo, da cibiyar kiwon lafiya matakin farko (PHC), da masallacin tsakiya, da kuma manyan matsugunai.
Da yake zantawa da wakilinmu, Hakimin Kauyen na Gbata, Alhaji Zakari Yahaya, ya ce wani da ba a bayyana sunansa ba ne ya bayar da gudunmuwar rijiyar shekaru biyar da suka gabata a lokacin barkewar cutar amai da gudawa a yankin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
A cewarsa, tun da rijiyar burtsatse ta lalace, kiraye-kirayen da aka yi wa gwamnati da kuma wakilan yankin da aka zaba domin a gyara shi ya ci tura, har sai da matan da suka ci gajiyar tallafin kudi suka kawo musu dauki.
Ita ma shugabar kungiyar mata, Zainab Ishaku ta shaida wa wakilinmu cewa tana da ra’ayin kawo sauyi a cikin al’umma tare da sanin irin wahalhalun da mata suka shiga na neman ruwan sha.
Ta ce tun lokacin da aka shigar da su cikin shirin Canjin kudi na sharaɗi a shekarar 2016, ta bullo da wata gidauniyar samar da kayayyaki ta cikin gida tare da tattara mata da su tanadin Naira 2,000 daga cikin Naira 5,000 da kowanne wata suke yi domin gudanar da aikin samar da ruwan sha a yankin.
Wata mace mai suna Misis Mary Isa da aka ga tana diban ruwa daga daya daga cikin famfunan al’umma, ta bayyana farin cikinta na samun ruwa mai tsafta a kauyensu ba tare da wata matsala ba bayan shafe shekaru da dama tana fama da wahala.
Shugaban makarantar firamare ta LEA, Mista Musa Ogye, da jami’ar PHC, Misis Hauwa Musa, sun tabbatar da cewa rayuwa ta yi matukar wahala ga al’ummar yankin sakamakon karancin ruwa har sai da matan suka shiga tsakani.
Shugabar Sashe na Shirin Canjin Kudi na Jihar Nasarawa, Misis Rhoda Agbawo, ta yi kira da a dore da cigaban shirin domin rage radadin talauci.
Ta kuma shawarci sauran wadanda suka ci gajiyar shirin da su kwaikwayi matan Gbata ta hanyar yin amfani da wani bangare na kudaden alawus dinsu na wata-wata don gudanar da ayyukan rayuwa mai dorewa.