Yanzu haka dai, jama’a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da wani faifayin bidiyo da aka yada ta shafukan Intanet, inda aka ga wasu yara matasa na dukan kawo-wuka ga wasu ‘yan mata a garin Bauchi.
Lamarin dai ya sanya shugabannin al’umma, malaman addini tare da kungiyoyin kare hakkin dan-adam zafafa kiraye kirayen sai lallai jami’an tsaro, sun kamo wadanda suka yi wannan aika-aikar.
Tuni rundunar ‘yan sandan jihar Bauchin ta baza koma domin ganin ta kamo wadannan matasan da ake zargi.
ASP Ahmad Wakili, Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce rundunar ‘yan sandan na nan na bincike domin gano wadannan matasan da suka aikata wadannan aika-aika na yiwa wadannan mata dukan kawo wuka harda aske musu gashin kansu.
Halima Musa mai shekara 17, da Faiza Isiyaku mai shekaru 20, suna daga cikin matan da wannan ibtila’in ya afka musu. Sun ce su ba abin da suka yi musu. Amma wata budurwarsu ce take fada da Halima. Inda ta ce ita ce ta kira su Unguwarsu, inda suna zuwa sai ta gayyato wadansu ‘yan sa kai suka afka musu.