Wasu tsageru sun ƙone ofishin ‘yan sanda na Aboh Mbaise da ke Jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.
‘Yan bindigar sun cinna wa caji ofis ɗin wuta ne a jiya Alhamis ta hanyar wurga abubuwan fashewa cikinsa.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Orlando Ikeoku, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun yi musayar wuta da maharan kafin daga baya su tsere.
Rahotanni sun ce ba a daɗe da sake gina ofishin ba biyo bayan cinna masa wuta da aka yi a loƙacin zanga-zangar EnSARS a shekarar da ta gabata.
Ya ƙara da cewa duk da babu wanda ya rasa ransa amma wani ɗan sanda ya ji rauni.
Ranar Laraba ma wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda huɗu a wani wurin binciken ababen hawa a kusa da Calabar, babban birnin Jihar Cross River da ke kudancin ƙasar.
Kazalika, maharan sun sace makaman jami’an tsaron.