Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wasu yara masu ƙananan shekaru bisa zargin yin garkuwa da wata ƙaramar yarinya mai shekara 6 a duniya.
A cewar ƴan sandan, sunayen waɗanda ake zargin sune Abdulrazak Ibrahim, Aliyu Salisu, daMohammed Ibrahim, sannan dukkan su ƴan shekara 19 a duniya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: An samu akasi: Kwalliyar wata amarya ta janyo cece-kuce
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, a wata sanarwa ranar Laraba, yace waɗanda aka zargin sun haɗa baki sannan suka sace yarinyar a Bachirawa Kwatas, jihar Kano, a ranar 6 ga watan Janairun 2023.
Isah ya kuma bayyana cewa waɗanda ake zargin sun buƙaci da a basu Naira miliyan biyu (₦2m) a matsayin kuɗin fansa.
Kakakin yace an cafke ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin a wurin karɓar kuɗin fansan.
Gambo Isah ya bayyana cewa:
“Sun sace wata yarinya mai suna Fatima Abubakar, ƴar shekara 6 a duniya, wacce ke a Bachirawa Kwatas, jihar Kano, a ranar 6 ga watan Janairun 2023 da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe, sannan suka tafi da ita zuwa jihar Katsina, inda suka buƙaci a basu Naira miliyan biyu a matsayin kuɗin fansa.
“Wanda ake zargin (Aliyu Salisu wanda ake kira da “Chilo”) ya shiga hannu ne lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansar.”
“Yayin gudanar da bincike, an cafko sauran waɗanda ya haɗa baki da su sannan aka ceto yarinyar ba tare da ko kwarzane ba.”
Za a Yi Zabe Kamar Yadda Aka Tsara, Buhari Ya Tabbatar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a gudanar da zabe mai zuwa kamar yadda aka tsara.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar Bishop-Bishop na Najeriya (CBCN) a fadar gwamnati da ke Abuja.
An dai ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta kan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi a ranar Litinin da ta gabata cewa zabukan na bana na fuskantar barazanar sokewa ko dage zabe matukar ba a magance matsalar rashin tsaro a sassan kasar nan ba.