Wata kungiya mai zaman kanta dake da ofishi a Kaduna mai suna Arida Relief Foundation tare da hadin guiwar jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar ‘yanto wata mata mai suna Hassana Sale wacce aka rufe ta a daki mai duhu har na tsawon shekara biyu a gidansu domin ganin hana ta haduwa da mijinta.
Matar rahotanni sun bayyana cewa ‘ya’yanta hudu da mijin, kuma jami’an ‘yan sanda da kungiyar sun same ta ne cikin wani mawuyacin hali a wani daki mai duhu a cikin gidansu a ranar Litinin a garin Rigasa a jihar Kaduna.
Shugabar kungiyar, Hajiya Rabi Salisu, ta ce matar mai suna Hassana Sale, yayanta mai suna Malam Lawal ya danne mata ‘yancinta na kokarin da ta yi wajen komawa gidan mijinta.
Rabi Salisu ta ci gaba da cewa; a lokacin da aka sake ta, matar ta kasance cikin halin bakin ciki, amma sakamakon soyayyarta ga ‘ya’yanta, ta kan kai musu ziyara a koyaushe. “tana kai wa yaran ziyara a kusan kowacce rana, wannan dalilin ya sanya yayanta da kuma wadansu ‘yan’uwanta suka rufe ta a wani daki mai duhu har na tsawon shekara biyu domin kange ta daga komawa wurin tsohon mijinta.” In ji Rabi Salisu da take shaidawa manema labarai hakan a Kaduna.
Ta kara da cewa; sun dauke ta sun kai ta asibiti, inda ta ce idan ta dawo hayyacinta za a mika ta zuwa ga ma’aikatar jin kai domin ci gaba da binciken lamarin.
Ya zuwa hada rahoton, tuni jami’an ‘yan sanda suka cafke yayan na ta.