Wani biditon wata baturiya tana ba mijinta ɗan Najeriya abinci a duƙe, ya sanya mutane da dama sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi.
Baturiyar a cikin bidiyon da aka sanya a TikTok, an nuna ta ɗauke da tire cike da. abincin sa, sannan ta durƙusa kan guiwoyinta yayin da ta ɗora abincin kan teburi a gaban mijinta, rahoton Legit.ng ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Tinubu Ya Dage Kan Yankin Da Yake Son Ya Shugabanci Majalasar Dattawa Ta 10
Can kuma sai ta ɗauko kwanon ruwa cikin murmushi yayin da mijinta ya wanke hannun sa a ciki. Daga bisani kuma sai ta zauna kusa da shi tana goge masa baki yayin da ya ke cin abincin.
Bidiyon wanda baturiyar ce ta sanya shi, ta rubuta cewa:
“Ba maigidana abincin dare.”
Lokacin da wani ya zarge ta da neman suna da bidiyon, inda ace ba haka ta ke yi ba a bayan kyamara, sai ta kada baki tace:
“Ina gayyatarka ka zo gidana ka tabbatar ok.”
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin abinda mutane su ke cewa akan bidiyon:
Jacob Tsolo ya rubuta:
“Namiji yana son a karrama shi, hakan zai sanya ya riƙa dawowa gida da wuri duk inda ya ke.”
glock4064 ya rubuta:
“Ni bana ma son mace ta yi min hakan amma har yanzu na kasa samun wannan mutuntawar.”
orashagraham ya rubuta:
“Ina buƙatar irin hakan a rayuwata, Dan Allah a wane kanti ka siyo ta?”