Bayan wani da ake zargin dan fashin ne ya kai farmaki gidan wata mata, da sannu ya gane cewa ya gamu da gamonsa, TheCareerbd.com ta ruwaito.
Ita ma ashe tana da makami amma ba bindiga ba, sai dai ya sha bakar azaba daidai gwargwado. Larondrick Macklin mai shekaru 31 ya afka wani gida da ke kudu maso yamman Decatur, Alabama a ranar Alhamis.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta samu faɗuwa ta fuskar cin hanci da rashawa
Macklin yana rike da karamar bindiga bayan ya shiga gudan da ke Wimberly, kamar yadda Newsweek ta ruwaito. Ana zargin gidan tsohuwar budurwarsa ce.
Yayin da Macklin ya shiga da karamar bindigarsa, wata mata wacce ta kasa samun makamai sai ta fara tunanin yadda za ta bullo masa.
An samu bayani kan yadda ya yi kokarin balle karafan tagarta, daga nan ta samu man girki mai zafi ta hukunta shi da shi.
Ba ta nuna wani imani ba ta watsa masa man ja mai zafin gaske a fuskarta don taimakon kanta da kanta.
Nan da nan fuskarsa ta babbake wanda ya rike fuskar ya rasa inda zai saka kansa har ‘yan sanda suka isa bayan an kira shi.
Yayin da suka isa ne suka garzaya da shi ofishinsu da ke Decatur. Bayan nan ne aka kai shi asibiti inda aka wanke masa ciwon amma duk da haka an sakaya shi a gidan yari.
Sannan ba a dora wa matar wani laifi ba saboda da yanzu Macklin ya yi mata lahani. Duk da dai wasu na zargin tsohuwar budurwarsa ce amma har yanzu ‘yan sanda basu gano akwai wata alaka tsakaninsu ba.
Likita ya sukurkuta halittar fuskar budurwar da ta je don ya ƙara mata tsawon hanci
Wata budurwa ta bayyana a bidiyo tana rusa kuka tare da ba mutane shawarar kiyayar likitocin Jihar Legas sakamakon ayar da ta gani a kanta, Legit.ng ta ruwaito.
Ta bayyana ne inda ta bayyana yadda likita ya lalata mata fuska inda ya mokadar da hancinta ta koma abar zunde a cikin jama’a.
Ta shaida cewa saurayinta ne ya matsa mata kan sai ta yi aikin idan ba haka ba sai rabu da ita matsawar ta ki amincewa.
Budurwar ta shawarci mutane kan cewa kada su kuskura su tafka irin nata kuskuren kasancewar maimakon a mikar mata da hanci ya kara kyau, sai aka mokadar da shi ya yi kudu.