Yadda wata mata ta hallaka Shugaban Ofishin ta kan yunƙurin cin zarafin ta
Ms Muhibat Taiwo Abdulsalam, Ma’aikaciyar Hukumar Kare Gasar Cin Hanci da Rashawa ta Tarayya FCCPC reshen Katsina, ta kashe maigidanta a ofishinsa da rana, inda ta zarge shi da yin lalata da ita.
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, Muhibat ta samu takaddamar kudi da Shugaban nata, Julius Haruna, Jami’in shiyyar Arewa maso Yamma, FCCPC a ranar data kashe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Yan bindiga Sun Farmaki Ayarin Motocin Uwargidan Gwamnan Jihar Osun
Wasu abokan aikinsu a ofishinsu ba su sani ba, Muhibat ta je ofishin ƴan sanda na GRA Katsina domin kai ƙarar Shugaban nata bisa laifin cin zarafi.
Muhibat wadda ita ce shugabar sashen koyar da masu amfani da kayayyaki na Hukumar da ke Katsina, an ce ta dawo ofishin da ke Unguwar Modoji, bayan Sallar Zuhur, tare da wasu jami’an ƴan sanda guda biyu don gayyatar shi domin yi masa tambayoyi, amma abin takaici sai dai gawar sa kwance a ƙasa, da tufafinsa a yage da gyale a saman jikinsa.
DAILY POST ta tattaro cewa Julius Haruna, mai shekaru 57, ya kai karar Ms Muhibat da yawa ga babban ofishin su kan rashin yin aikin daya dace.
Da yake tabbatar da rahoton rasuwar Jami’in FCCPC na shiyyar, Aegidius Haruna, ya ce “daga bayanin da na ji da kuma abin da na ji, sun yi rigima ne a kan kudin da aka amince mata a ofishin saboda tana bukatar karin wanda ya ki amincewa. Ina ganin haka matsalar ta faro.
“Mun kadu da mutuwarsa. ‘Yan uwanmu sun aiko ni nan don neman adalci a kan mutuwarsa, “in ji Aegidius a cikin wata taƙaitaccen bayani.
Sabanin haka, Muhibat a nata bangaren tana zargin marigayi maigidanta da akawun ofishinsu da yin lalata da su, tare da nuna rashin sanin mutuwar sa kafin ta garzaya zuwa ga ƴan sanda domin neman kariya daga waɗanda suka kai mata hari, kamar yadda wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ta bayyana.
Wasu majiyoyi da suka yi ikirarin ganin Muhibat bayan ta samu rakiyar ’yan sanda zuwa ofishinsu sun ce ta ga kamar ba takalmi ba kamar yadda tace marigayin ya kai mata hari.