Wata ‘yar Najeriya da ta yi rashin begen zama uwa ta yi maraba da jaririnta data haifa tana da shekaru 71,Legit.ng ta rawaito.
Matar ta yi farin ciki matuka a lokacin da ta baje kolin lafiyar jaririnta, inda ta ce ta haihu ba tare da wata matsala ba kuma cikin mintuna 10.
KARANTA WANNAN LABARIN:Oba Na Benin Ya Tunbuke Rawanin Wani Basaraken Gargajiya
Yayar Sabuwar Mahaifiyar ta ce anti ta yi aure tana da shekara 50 kuma tayi jira na tsawon shekaru 21 kafin ta haifi danta.
Tsohuwar ‘yar shekara 71 a Najeriya na cikin wani yanayi na biki bayan da ta yi maraba da jaririn nata bayan shekaru 21 da yin aure.
Uzo Oge, ‘yar uwar sabuwar mahaifiyar, ta ziyarci matar a gidanta da ke Fatakwal tare da mahaifiyarta don yin albishir.
Da take daukar ziyarar ta kyamara, Oge ta bayyana a wani faifan bidiyo na TikTok cewa kakarta ta yi aure tana da shekara 50 kuma ta rasa duk wani fatan haihuwa.
Sabuwar uwa da taji dadi ta kasa dauke farin cikinta domin ta godewa Allah cikin harshenta da turanci.
“Ubangiji kawai ya yi,” ta yi kururuwa tare da ware hannayenta a cikin iska. Ita ma ‘yar uwarta ta shiga bikin.
Ta kai su cikin gidanta don ganin yarinyar da aka haifa cikin koshin lafiya da ta fito ba tare da wata matsala ba.
Da take dauke da jaririyar a hannunta, mahaifiyar Oge ta tambayi jaririn a ina ta kasance duk wannan lokacin. Cewar sabuwar uwa, ta haihu cikin kasa da mintuna 10.
A wani labarin kuma, Gwamna Buni Ya Yi Alhinin Mutuwar Mutane 3 Da Wasu 6 Suka Jikkata A Wani Hatsarin Mota
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi alhinin rasuwar mutane uku da wasu shida da suka samu raunuka da dama a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Potiskum zuwa Bauchi.
Gwamna Buni a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mamman Mohammed ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana hatsarin a matsayin abin ban tsoro.