Wata budurwa Yar Nigeria Mai suna Paris Oma ta shiga kafar sada zumunta na zamani, inda ta bayyana a abun da saurayin ta yasa ta yi, bayan ta nemi naira dubu biyu daga gareshi.
A cewar Oma, a kafar sada zumunta ta na Facebook, ta bayyana cewa, Da ta bukaci saurayin ta, ya ba ta ta naira 2,000, sai ya ce ma ta bai da shi.
Kazalika Oma ta kara da cewa, saurayin na ta, ya kirata inda ya ke aikin, kuma ya sanya ta aiki har na kusan tsawon awa guda, kafin daga bisani ya dauki kudin da take bukata ya ba ta
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Oyo ya bayyana Litinin a matsayin ranar hutun ma’aikata
Lokacin da ta sanya hotunan aikin da ta keyi a wurin wani aikin Gini ta rubuta cewa;
“Na tambayi saurayina ya bani wasu kudi, sai ya cemun bai da shi, kuma da na bukaci dole sai ya ban, sai ya ce nazo wurin da ya ke aiki, don bantaba tunanin zai bani cebur na yi aiki ba ne, sai ya bani na yi mai aiki har na kusan awa guda, kafin ya bani naira dubu biyun da na bukata daga wurin shi” inji ta.
Ta kuma ce, ” Kaiiiiii abun ba sauki don sai da nakusan suma kafin ” a cewar ta.
A wani labarin Kuma na daban.
Farin ciki ya mamaye garin Minna bayan sanar da Tanko Beji a matsayin sabon angon jam’iyyar PDP reshen Jahar Neja.
Mataimakin gwamna jahar Benue Mr Benson Abuonu, ya sanar da yin nasarar lashe zaben.
Mr Benson Abuonu, ya bayyana yadda lamarin ya wakana inda yace Tanko Beji yayi nasara da kuri’u 2095 a cikin 2305, inda abokin hamayyar nasa Alhaji Muktar Ahmed ya samu kuri’u 95 kacal.
Jim kadan bayan sanar da zaben, yayan jam’iyyar PDP suka kidime da murna, suna nuna godiyarsu ga Malaman zaben kan yin kokarin gudanar da lamarin tsakani da Allah.
Tanko Beji ya nuna godiyarsa matuka bisa yadda alumma suka nuna masa kauna da goyon bayan su.
Ya kuma yi Kira ga al’umma kan cewar wannan ne lokaci mafi kamata da su hada kan su don fuskantar kalubalen dake tunkarar su a zaben 2023 mai zuwa.
Yace dole sau mun hadu don kawar da cin kashin da jam’iyyar APC ke yiwa al’umma a wannan lokaci.
Daga cikin manyan da suka halarci taron sun hada da Farfesa. Jerry Gana, tsohon Ministan yada labarai; a tsohon gwamnan Jahar Nejar. Shem Zagbayi Nuhu; Maajin jam’iyyar PDP na kasa Mista Maibasira; Senato Zaynab Kure, Alhaji Umar Mohammed Nasko.
Duk da mamakon ruwan da ake lafta a yayin gudanar da zaben dayawa jama’a sun daure ba su gudu ba.