Wasu ‘yan bindiga sun sace dan jarida da ke aiki da kamfanin jaridar PUNCH mai suna Okechukwu Nnodim, a gidansa da ke a kan titin Arab, a unguwar Kubwa, Abuja a daren ranar Laraba.
Yan bindigar sun kuma farmaki makwabtansa, inda suka yi awon gaba da yara biyu na wata bazawara mai suna Mrs Faith Gbeyide.
Da ta ke labarta yadda lamarin ya faru a ranar Alhamis, matar Nnodim mai suna Oluchi, ta bayyana cewa lokacin da ‘yan bindigar suka zo, mijinta na aiki a saman Kwamfutar shi, inda suka haura katanga tare da umurtarsu su bude kofar shiga cikin gidan.
Ta ce ‘yan bindigar sun yi harbi a jikin tagar gidan, daga bisani kuma suka balle karafan da suka tokare kofar, tare da balle kofar, suka shiga cikin gidan.
“Mijina ya umurce ni na zauna tare da yaranmu a dakinsu. Ina jinsu mutanen suna tambayar mijina ya fito masu da kudi, shi kuma ya fada masu cewar ba shi da kudi a cikin gidan.
“Sun kwashe mana wayoyinmu tare da yin awon gaba da mijina. Haka zalika sun shiga gidan makwabciyarmu inda suka tafi da yaranta guda biyu.”
Madam Gbeyide ta bayyana cewa yaronta ne ya bude kofar gidan bayan da suka yi barazanar kashe su gaba daya idan har suka shiga ciki.
Ta bayyana cewa, “Sun sace N9,000 da ke cikin jakata, suka kuma dauke talabijin din da ke cikin dakina tare da yin awon gaba da yarona. Yaro na na biyu sai ya fara binsu yana kuka, inda shi ma suka tafi da shi.”
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ASP Miriam Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin.