An sace wani Hakimi a jihar Adamawa a daren Litinin din da ta gabata bayan sabon Kwamishinan ‘yan sanda ya sha alwashin rage aikata laifuka.
Sabon kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Adamu, ya kira wani taron manema labarai da misalin karfe 11 na safiyar Litinin a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar da ke Jimeta, Yola.
Yayin da ‘yan bindigar suka dauke hakimin Mayo-Farang a karamar hukumar Mayo-Belwa, Mustapha Ahmadu, a kewayen tsakar dare na wannan rana, The Nation ta ruwaito.
Bayanai sun ce an sace Hakimin, wanda yake matsayin Sarkin Noman Adamawa, ‘yan sa’o’i kadan bayan ya dawo jihar daga Abuja.
A cewar bayanan, ‘yan bindigar sun far wa fadar ne da tsakar daren ranar Litinin inda suka yi awon gaba da shi bayan sun rinjayi masu gadin fadar.
“Duka garin ya kasance cikin tashin hankali yayin da harbe-harben bindiga ke hayar iska da tsakar dare. An sace hakimin duk da kasancewar masu gadin fadar, ”inji daya daga cikin majiyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Adamawa (PPRO), DSP Suleiman Nguroje, ya ce rundunar ta tura jami’anta don ceton hakimin tare da cafke ‘yan bindigar.