Jami’an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun tabbatar da sace daliban makarantar sakandire ta gwamnati a garin Kaya dake jihar ta Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar cewa da safiyar jiya Laraba ‘yan bindiga suka farmaki makarantar dake Karamar Hukumar Maradun.
“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara na sanar da sace daliba 73 na Makarantar Sakadiren Gwamnati a garin Kaya dake karamar Hukumar Maradun. Gungun ‘yan bindigar sun sace daliban ne da misalin karfe 11 na safiyar Laraba.” Inji Jami’in Hulda da Jama’a Na Rundunar ‘Yan Sandan.
Jami’in ya bayyana cewa hukumarsu ta fara aikin hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da an ceto daliban daga hannun ‘yan bindigar, kuma tuni rundunar ta su ta kai jami’a kewayen garin da abin ya faru.