Sabbin bayanai daga jihar Kogi na nuni da yadda wasu gaggan ‘yan fashi dauke da muggan makamai suka hallaka jami’an ‘yan sanda takwas cikinsu kuwa har da mai mukamin DPO bayan sun afka wa bankin First Bank da ke garin Isanlu a jihar.
Ya zuwa hada wannan rahoton babu cikakken bayani game da lamarin da kuma adadin rayukan da suka salwanta, amma bayanai sun nuna cewa ‘yan fashi sun kashe hatta wasu daga cikin ma’aikatan bankin da kwastamominsu.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya dai ta bayyana cewa ta dukufa wajen gudanar da cikakken bincike kafin ta yi karin bayani game da lamarin.