Kasuwar Kantin Kwari da kewaye a jihar Kano ta cika da ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.
A baya-bayan nan dai ana fama da ambaliyar ruwa a fadin Najeriya, kuma jihar Kano ta sha fama da da hakan a lokuta da dama.
Karanta kuma: Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gada Da Gidaje A Yobe
A Kano, ‘yan kasuwa a shahararriyar Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano sun yi asarar kayayyakin da suka kai sama da Naira miliyan 200 da shaguna da rumfuna sama da 300, sakamakon haka.
Daily Trust a rahotonta na Daily Nigerian a yau, ta gano yadda lamarin yake, da kuma me hukumomi ke yi a kai?
A wani labarin kuma: Mutane Da Dama Sun Makale, Yayin Da Gini Ya Rufta A kasuwar Kano
Wani gini da ake ginawa ya ruguje a daya daga cikin kasuwannin sai da wayoyi wato GSM Market dake garin Kano na jihar Kano.
Ginin yana kan titin Beirut, wani yanki mai cike da jama’a a Kano.