An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Hon Abok Ayuba Nuhu.
An maye gurbinsa da Sanda Yakubu, wanda ya fito daga mazabar Pingana ta karamar hukumar Bassa ta jihar.
Mambobi 16 daga cikin 24 na majalisar ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi a zauren majalisar a ranar Alhamis..
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa an fara yada jita-jita game da tsige Abok ne mako guda da ya gabata inda aka rika yada jita-jitar da manema labarai da rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Tsaro sun Manaye Zauren Zauren Majalissar Filato
A ranar Alhamis da misalin karfe 5:30 na safe ‘yan majalisar ciki har da na jam’iyyar PDP suka hallara a zauren majalisar.
‘Yan majalisar dai sun kusa yin musayan hannune ne a lokacin da aka gabatar da batun tsige shi.
Yan jam’iyyar PDP wadanda ke biyayya ga shugaban majalisar sun dauki sandar domin hana tsige shi.
Amma ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke da rinjayen tsige shi, sun ja sandar suka sanya ta a mazauninta, suka ci gaba da yunkurin su..
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kafin ’yan majalisar su yi dafifi a gidan, jami’an tsaro sun tare hanyar da za ta bi wajen taron.
Kazalika ta ruwaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin Gwamna Simon Lalong da tsige shugaban majalisar bayan harin da aka kai a unguwar Yelwan Zagam da ke yankin Jos ta Arewa, inda aka kashe mutane.
Bayan harin, kakakin majalisar ya fara sukar gwamnan jihar a fili.
Ya kuma daina halartar ayyukan gwamnati a jihar
Comments 1