By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta tabbatar da cafke wani likita mai suna Dokta Christian Osakwe bisa zargin yi wa ‘yar aikin sa fyade a garin Asaba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata a Asaba cewa an kama Osakwe tare da tsare shi a gidan yari bayan da ‘yan sanda suka kai kara kan zargin.“A halin yanzu wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda a SCID, kuma mun fara bincike kan zargin.
“Ina tabbatar muku da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu,” inji Edafe.
Wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Mista Harrison Gwamnishu, wanda ya shigar da karar a gaban ‘yan sanda, ya shaida wa manema labarai a Asaba cewa wanda ake zargin ya ba shi Naira miliyan 1 don ya janye karar.
Yace wanda ake zargin shi ne Babban Daraktan Lafiya (CMD) na Asibitin Victory and Maternity Home, wanda ke kan titin Kings, Umuaji Quaters, Asaba.
A cewar Gwamnishu, ana tuhumar Osakwe da laifin yiwa yar aikin gidan sa fyade da kuma wata ‘yar kanwar matarsa.
“Haka zalika, a wani faifan bidiyo daga bincikenmu na sirri, mun gano cewa shi ma yana lalata da ‘yar ‘yar uwar matarsa.
“Da farko dai ya musanta dukkan zarge-zargen amma daga baya ya amsa laifin lokacin da muka tunkare shi da hujjoji.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Ya yi tayin biyan jami’an kudu naira miliyan daya domin su janye maganar, amma suka ki amin cewa. Inda suka ce “Duk da haka, mun yi nasarar mika wanda ake zargin da Naira miliyan 1 ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike,” in ji Gwamnishu.